Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham na shirin sayen Alvaro Morata don maye gurbin Harry Kane, dan wasan da ke kokarin raba gari da kungiyar a karshen wannan kaka bayan gaza cimma jituwar sayar da shi a kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata.
Shugaban Tottenham Fabio Paratici ya ce dan wasan mai shekaru 28 na jin dadin zamansa a kungiyar yanzu haka, duk da dambarwar da ta dabaibaye shirin sayar da shi a kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata.
Sai dai sanarwar da Tottenham ta wallafa a shafinta ta ce tana fatan sayen Morata wanda yanzu haka ya ke taka leda da Juventus matsayin aro daga Atletico Madrid.
A baya-bayan nan ne Kane ya bukaci Tottenham ta yi gyara a kwantiraginsa don bashi damar iya raba gari da kungiyar gabanin karewar kwantiraginsa tare da kayyade kudin sakinsa kunshe a kwantiragin don saukaka cinikinsa.
A wani labarin na daban kaften din Ingila Harry Kane ya ce, zai ci gaba da zama a kungiyarsa ta Tottenham a cikin wanann kaka, yana mai jaddada cewa, dari bisa dari, nauyin taimaka wa kungiyar na samun nasara, ya rataya a wuyansa.
Manchester City dai, ta kagu ta kulla yarjejeniya da Kane wanda take ganin zai raba gari da Tottenham a cikin wannan kakar.
Sai dai shugaban Tottenham Daniel Levy ya ki zaman tattaunawa da Manchester City don cimma matsaya kan cefenar da Kane mai shekaru 28.
Tuni Kane ya yi wasansa na farko a cikin wannan sabuwar kakar gasar firimiyar Ingila a ranar Lahadi bayan ya fara yin zaman banci kafin daga bisani ya shigo wasan wanda suka doke Wolves da ci 1-0.