Kungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da shirin fadada ayyukan sojinta a Somalia don kakkabe duk wata kungiyar da ke alaka da Al-Qaeda dai dai lokacin da wa’adinta na farko a yakar kungiyar ta’addanci ke shirin karewa a ranar 31 ga watan Disamba.
Kungiyar ta AU ta bukaci Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya duba yiwuwar kara aikin rundunar ANISOM wanda ke dauke da sojoji dubu 20 a cikin kasar ta Somalia.
A wani labarin na daban kashe-tashen hankulan da kasar Somalia ta jima ta na fama da shi, ya yi sanadin baiwa kungiyar ta’addanci ta Al Shebaab damar samun gindin zama tare da cin karenta babu babbaka.
Mayakan Al-Shebaab sun kai farmaki kan wani sansanin sojojin Somalia, inda kuma suka sake karbe iko da wani gari da dakarun gwamnatin kasar suka kwace daga hannunsu a farkon wannan watan da muke ciki.
Kodayake rahotanni sun ce, tuni sojojin suka mayar da martani ta hanyar yi wa mayakan luguden wuta ta sama.
Ko a cikin watan Afrilu, Al Shabab ta bayyana cewa ta kai hare-hare rabin dozin, ta ce ta kashe sojojin kungiyar tarayyar Afrika 59 mafiya yawansu kuma sojojin kasar Uganda ne, a yayin da su kuma suka ce an kashe masu rasa mayaka 14.
Daga nasu bangaren Dakarun Uganda sun bayyana mutuwar sojojinsu 4 ne, ba kamar yadda al Shebab ta sanar ba, a yayin da su ka ce sun kashe mayakan na Shebab 22.
Mafi yawan hare haren dai, an kai su ne ta hanyar harba rokoki kan sansanonin sojin samar da zaman lafiyar na Amisom dake da sansani a yankin na Bas-Shabelle.