Taliban ta sanar da shirin baiwa mata damar komawa makarantu a nan gaba kadan, biyo bayan caccakar da ta fuskanta daga kasashen duniya sakamakon dakatar da matan zuwa makarantu da kuma wuraren aiki.
A cewar kakakin yanzu haka suna tattaunawa kan yadda karatun matan zai ci gaba da wakana da kuma ayyukan da ya kamata su yi a sassan kasar ta Afghanistan bisa matakan kare dokokin addinin Islama.
Sai dai kakakin ya nanata shirin tafiyar da gwamnatin Taliban da Maza zalla ba tare da sanya mata a harkar tafiyar da gwamnati ba, lamarin da ya janyo cecekuce musamman daga manyan kasashen Duniya.
Duk da alkawurran da ta dauka na gudanar da mulki ba tare da take hakkin dan adam ba, akwai fargabar Taliban ta iya komawa turbar yadda ta jagoranci Afghanistan a shekarun 1996 zuwa 2001, lokacin da ta haramtawa mata karatu da aiki, da kuma hana su fita face tare da muharramai, musamman bayan matakan baya-bayan .
Taliban ta bayyana cewa ta na bukatar karin lokaci gabanin kammala tantance yadda za ta tsara karatu da aikin mata da zai yid ai dai da tanadin addinin Islama, inda Mujahid ke cewa zamani ya sauya don haka dole su samar da tsarin da dokokin addini suka amince da su.
Antonio Guterres ya ce akwai bukatar manyan hukumomin duniya da kasashe su mu’amalanci Taliban kasancewar hadari ne kaurace mata, wanda kuma zai iya kai wa ga karasa ruguza kasar baki daya.
Guterres na wadannan kalamai ne ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taro kan wata gidauniya da aka kaddamar da nufin taimaka wa jama’ar Afghanistan.
A cewar sa sanya idanun kasashe duniya da kuma yin mu’amala da gwamnatin Taliban ne kadai zai ceto jama’ar kasar daga matsanacin talauci da yunwa da kuma kare su daga cin zarafin dan adam.
Taron da aka gudanar ranar Litinin, na da nufin samar da wata gidauniya da za’a tara akalla dala miliyan dari 6 don tallafa wa jama’ar Afghanistan da yanzu haka ke fuskatar matsanacin talauci da tsananin yunwa sakamakon tsayawar al’amurra cik, tun bayan da Taliban ta karbe iko da gwamnatin kasar.
Tun a tsakiyar watan Agusta lokacin da Taliban ta karbe iko da mulkin Afghanistan ne kasashe suka fara yanke hulda da Afghanistan da kuma cin alwashin kauracewa duk wata mu’amala da ita, abin da Guterres ke ganin cewa gurgiuwar shawara ce.