Daruruwan mutane ne suka shiga zanga zangar adawa da komawar tsohon Sarkin Spain Juan Carlos gida, wanda ya koma kasar daga Daular Larabawa inda ya kwashe shekaru 2 yana gudun hiira.
Kakakin gwamnatin Spain yace akalla mutane 300 suka gudanar da zanga zangar kusa da fadar Sarkin dake madrid domin nuna bacin ran su saboda zargin cin hanci da kuma halarta kudaden haramun da ake masa.
Wannan Litinin ake saran tsohon Sarkin ya ziyarci dan sa Sarki Felipe na 6 kafin komawa Daular Larabawa inda yake zama.
Gwamnatin Firaminista Pedro Sanchez na ci gaba da dakon bayanai akan dalilin da ya sa Juan Carlos ya sauka daga karaga a shekarar 2014 domin nada dan sa.
A wani labarin na daban firaministan Spain Pedro Sanchez ya sha alwashin haramta aikin karuwanci a kasar, wanda ya bayyana shi a matsayin bautar da mata.
Yayin da yake tsokaci a wajen rufe taron jam’iyyar sa na kwanaki 3 da akayi a Valencia, Sanchez ya bayyana manufofin da gwamnatin sa ta gabatar wadanda yace sun taimaka wajen shawo kan rikice-rikicen da ake samu da kuma batun karin albashi.
Firaministan ya yiwa mahalarta taron alkawarin cewar zai aiwatar da shirin haramta karuwancin a fadin kasar saboda abinda ya kira yadda mummunar dabi’ar ke zama kamar bautar da mata.
Ya zuwa yanzu dai babu wata dokar da ta hana biyan kudi a bainar jama’a domin daukar matar da za’ayi lalata da ita, sai dai dokar da ta hana safarar mata.
Dokokin Spain basu amince da karuwanci a matsayin aikin yi ba, amma kuma akwai gidajen karuwai da dama a fadin kasar, inda wasu ake samun su a matsayin otel, wasu kuma gidajen kwana ne kawai.
Hukumar binciken kasar Spain tace akalla kowanne mutum guda a cikin mazaje 3 dake kasar ya taba biyan kudi akalla sau guda a rayuwar sa domin yin lalata da mace kamar yadda wani binciken da aka gudanar a shekarar 2009 ya nuna.