Shugaban gwamnatin Sojojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana mambobi 93 na sabuwar majalisar rikon kwaryar kasar, watanni biyar bayan ayyana kansa a matsayin shugaba, sakamakon rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno.
Akwai dai masu adawa da tsohon shugaba Deby cikin membobin majalisar dokokin rikon kwaryar ta Chadi, sai dai babu mamba ko guda daga cikin kungiyar ‘yan adawa ta Wakit Tamma, ko kuma daga kungiyoyin farar hula da suka yi tir da darewa shugabancin Chadi da karamin Deby ya yi.
Ranar 11 ga watan Mayu, gwamnatin Sojojin Chadi ta nada tsohon firaministan kasar Albert Pahimi Padacke, kan tsohon mukamin nasa amma na rikon kwarya.
Pahimi Padacke dai shi ne Firaminista na karshe a karkashin tsohon shugaban Chadi marigayi Idriss Deby Itno.
A wani labarin na daban kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnatin China dangane da yadda kasar ke cin zarafi tare da kuntatawa tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uighur.
A wani taron ministocin wajen kasashen 27 ranar Litinin mai zuwa ne takunkuman za su tabbata wadanda za su shafi hatta kasashen Rasha Korea ta Arewa da Eritrea da kuma Sudan ta Kudu baya ga Libya dukkaninsu saboda tuhume-tuhume ko kuma zargin take hakkin bil’adama.
Tuni dai China ta nuna bacin ranta game da yunkurin sanya mata takunkumai kan halin da ‘yan kabilar ta Uighur ke ciki a yankin Xinjiang inda jakadan kasar a EU Zhan Ming ke cewa Turai na shirin kakabawa Beijing takunkuman bisa kaffa hujja da kare-rayi baya ga rahotannin da basu da tushe.
A cewar Mr Zhan, China na bukatar tattaunawa ta fahimtar juna tsakaninta da EU amma kafin wannan yakamata Turai ta yi tunani sosai gabanin kakaba mata takunkuman wadanda za su shafi alakar da ke tsakaninsu, domin kuwa a acewarsa Beijing ba za ta zuba ido ba tare da daukar mataki ba.
Mr Zhan ya nanata cewa China ba ta da hannu a zargin da ake mata kuma a shirye ta ke ta mayar da martani kan duk wani yunkuri ko kuma barazana ga tsaro da manufofinta.