Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun harbe wani matashin Bafalasdine har lahira a wani samame da suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin gabar yammacin gabar kogin Jordan, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankunan da sojojin yahudawan ke ci gaba da kuntata wa al’ummar Falastinu.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, Younis Ghassan Tayeh, mai shekaru 21, an kashe shi ne a ranar yau Laraba a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Far’a, wanda ke kilomita hudu (mil 2.4) kudu maso yammacin birnin Tubas, bayan da sojojin yahudawa suka harbe shi a zuciya.
Bayanin ya kara da cewa likitocin Falasdinu sun garzaya da matashin zuwa asibiti a Tubas, amma sakamakon samun munan raunuka ya yi shahada ba da jimawa ba.
Sojojin Isra’ila sun kuma kutsa cikin wasu gidaje a wannan sansanin, lamarin da ya haifar da arangama tsakaninsu da Falastinawa mazauna yankin.
Sojojin yahudawan sun yi ta harbe-harbe da harsasai masu rai, da kuma harba da barkonon tsohuwa da kuma gurneti domin tarwatsa masu zanga-zangar.
A wani labarin na daban manzon Amurka na musamman Mike Hammer ya isa Habasha don tattaunawa da gwamnatin kasar a wani yunkuri na ganin an sulhunta bangarorin da ke yakar juna da nufin tsagaita wuta a sabon yakin da ya sake barkewa a karshen watan jiya.
A karshen watan jiya ne yaki ya dawo sabo tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen na Tigray a yankin arewacin kasar bayan da bangarorin biyu suka zargi juna da karya ka’idojin da ke kunshe a kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar da suka kulla.
Tun a karshen mako ne Amurka ta sanar da Hammer a matsayin jakadan wanda ta nemi ya yi aiki tukuru don farfado da fatan yiwuwar kulla yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawo rikicin bangarorin biyu.
Tuni dai aka yi wata ganawa ta musamman tsakanin Hammer da jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman Hanna Serwaa Tetteh da ke jagorancin shirin kawo karshen rikicin na Habasha.
Ko a ziyarar da ya kai watan jiya tare da Jakadan Tarayyar Turai Annette Weber, Hammer ya kai ziyarar gani da ido yankin na Tigray da yaki ya daidaita inda suka roki bangarorin biyu da su tabbatar da kawo karshen rikicin.
Bayanai dai sun ce Hammer zai yi ganawa ta musamman da Firaminista Abiy Ahmed, sai dai har zuwa yanzu babu bayani kan yadda ganawar za ta guda walau daga gwamnatin Habasha ko kuma Amurka.
Source; ABNA HAUSA