Majalisar Sojin Sudan ta sallami akala mutane 115 da ake tsare da su biyo bayan shiga zanga-zangar kyamar hukumomin. Kasashen Duniya na ci gaba da kira ga hukumomin soji na Sudan na ganin sun yi sassauci wajen tafiyar da ragamar iko.
Akasarin mutanen da aka sallama na aiki ne da kuyngiyoyin kare hakokin bil Adam na wannan kasa da ta fada rikicin siyasa tun bayan juyin mulkin da yayi gaba da gwamnatin Omar El Beshir.
Ana tsare da akasarin masu rajin kare hakkokin bil Adam ne ba tareda an zartas musu da hukunci ko tuhumar su da wani laifi a hukumance.
Majalisar sojin kasar ta sako wadanan mutane ne a wani lokaci da ya zo dai-dai da ziyarar manzon Majalisar dinkin Duniya da zai share kwanaki biyar a kasar ta Sudan.
Adama Dieng da sunan majalisar dinkin Duniya sashen dake kula da kare hakkokin bil Adam zai ganawa da majalisar sojin kasar,kazzalika zai yi amfani da wannan dama inda zai haduwa da wakilan kungiyoyin kare hakkokin bil Adam a Sudan,hanyar da zai yi amfani da ita domin sauraren wasu daga cikin koken su,musaman neman yanci gudanar da zanga-zanga da incin fadar albarkacin bakin su.
A watan yuni na wannan shekara ne manzon na Majalisar Dimkin Duniya dan kasar Senegal Adama Dieng zai gabatar da sakamakon bincike da aka yi a kasar biyo bayan kisan mutane 82 yayin zanga-zangar kyamar hukumomin wuccin gadi.
A wani labarin na daban Jami’an tsaro a kasar Sudan sun kama jagororin adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi wadanda ke wallafe wallafe a intanet cikin su har da tsohon minista daga kungiyar FFC ta fararen hula.
Rahotanni sun ce Yan Sandan farin kaya sun kama tsohon ministan Omar Youssef lokacin da yake jagorancin taro tare da Mohammed Hassan Arabi, wani babban jami’I a Jam’iyyar Congress Party.
Kama wadannan mutane na zuwa ne kwana guda bayan da wasu mutane biyu suka shiga tawagar da ta gana da wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Volker Perthes dake jagorancin yunkurin sasanta rikicin siyasar kasar.
Babban dan adawar kasar Yaseer Arman yace kama wadannan mutane na iya yin illa ga tattaunawar zaman lafiyar da Majalisar ke jagoranci.