Shugabannin Turai Suna Maraba Da Nasarar Macron A Zaben Faransa.
Shugabannin Turai suna maraba da nasarar Emmanuel Macron a wa’adi na biyu na shugabancin kasa, kuma suna bayyana nasarar da ya samu a matsayin babban ci gaba, wanda zai sanya Tarayyar Turai ta iya dogaro da Faransa na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi maraba da nasarar da Emmanuel Macron ya samu a wa’adi na biyu na shugabancin kasa.
Der Leine ta taya shugaba Macron murna a shafinta na Twitter, tana mai cewa: “Ina fatan ci gaba da kyakkyawar alaka da hadin gwiwarmu.”
Ta kara da cewa, “tare, za mu ciyar da Faransa da Turai gaba.”
A nasa bangaren, shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya ce bayan sake zaben Macron da aka yi: Kungiyar Tarayyar Turai za ta iya dogaro da Faransa na tsawon shekaru biyar a nan gaba.
Ministan kudi na Jamus Christian Lindner ya yi la’akari da cewa zabin da Faransa ta yi na Macron a matsayin shugaban kasa ya sa tarayyar turai ta kara samun wata bababr nasara.
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya taya shugaban Faransa Emmanuel Macron murnar nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa, yana mai cewa wadanda suka zabe shi sun aike da wani sako mai karfi na nuna goyon baya ga Tarayyar Turai.
Har ila yau, shi ma a nasa bangaren Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ya taya Emmanuel Macron murnar sake zabensa a matsayin shugaban kasar Faransa, yana mai nuna farin cikinsa na ci gaba da yin aiki tare da shi, yana mai jaddada cewa Faransa na daya daga cikin ‘yan kasashen da ke kusa da Burtaniya.
A cikin harshen Faransanci, Johnson ya wallafa a shafinsa na twitter cewa: “Ina taya Emmanuel Macron murnar sake zabensa a matsayin shugaban kasar Faransa,” yana mai cewa “Faransa na daya daga cikin kawaye mafi kusa kuma mafi muhimmanci.”
A nasa bangaren, firaministan Italiya Mario Draghi ya ce nasarar da Emmanuel Macron ya samu a zaben shugaban kasar Faransa, wani labari ne mai girma ga daukacin kasashen Turai.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, da kashi 58%, idan aka kwatanta da kashi 42% na Marine Le Pen, bayan zaben da aka gudanar a zagaye na biyu.