Shugaban Iran ;Kasashen Turai Ne Ummul-Haba’isin Ta’addancin Da’ish Da HKI.
Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isy ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa; Zaluncin da ‘Yan Sahayoniya suke yi wa masallata Falasdinawa a masallacin Quds, da laifukan da kungiyar Da’ish ta tafka akan mutanen da suke ciki halin salla a wani masallaci na kasar Afghanistan, kirkira ce ta kasashen turai da ‘yan sahayoniya.
Shugaban kasar na Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahadar Imam Ali ( A.S ), ya yi bayani akan cewa “sunnar Ubangiji ce ya taimakawa mutane masu rauni da wadanda ake zalunta.”
Shugaban kasar ta Iran Sayyid Ra’isy ya kuma ce; Shirin da aka yi na cewa za a warware matsalar Falasdinu ne ta hanyar tattaunawa akan teburi ya ci tura, don haka abinda yake faruwa a yanzu shi ne Masu jihadi ne za su ayyana makomar Falasdinu.
Dangane da ranar Quds ta duniya wacce ake yi a juma’ar karshe ta watan Ramadan, shugaban kasar ta Iran ya ce; Wannan rana ce ta hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi domin birnin Quds da masallacinsa.
READ MORE : London; Wasu Yahudawa Sun Kona Tutar Isra’ila A Gaban ofishin Firaminista.
READ MORE : Shugabannin Turai Suna Maraba Da Nasarar Macron A Zaben Faransa.