Shugabannin kasashen Iran da Rasha sun tattauna kan halin da ake ciki a kasar Afghanistan, da kuma sauran batutuwa da suka shafi alaka yarjejeniya kan shirin Iran na nukiliya.
A zantawar da suka gudanar a daren jiya, shugaba Ibrahim Ra’isi na Iran da kuma shugaba Vladimir Putin na Rasha, sun yi doguwar tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar Afghanistan, da kuma yadda za su hada karfi da karfe wajen yin aiki tare, domin tabbatar da cewa kasar ba ta wargaje ba.
Ra’isi da Putin sun jaddada wajabcin yin aiki tare a tsakanin kasashe makwabtan kasar Afghanistan domin ganin kasar ta samu zaman lafiya, da kuma hana barkewar duk wani rikici, wanda ka iya kai kasar ga yakin basasa.
Baya ga haka kuma shugabannin na Rasha da Iran sun tattauna batun yarjejeniyar nukiliya kan shirin Iran, da kuma muhimmanci sake farfado da wannan yarjejeniya, inda Ra’isi ya dora alhakin tsaikon da yarjejeniyar ta fuskanta a kan kasar Amurka da kuma sauran kasashen yammacin turai.
Ibrahim Ra’isi da kuam Vladimir Putin, sun jaddada wajabcin ci gaba da kara bunkasa alaka da kuma yin aiki tare a dukkanin bangarori tsakanin Iran da Rasha.
Kafin wannan lokacin a jiya, shugaban kasar China Xi Jinping ya tuntubi shugaba Ibrahim Ra’isi ta wayar tarho, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a Afghanistan, da sauran batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu.