Shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma sun fara gudanar da taron su na musamman a birnin Accra dake kasar Ghana, inda ake saran su tafka mahawara dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso da kuma yunkurin da bai samu nasara ba a Guinea Bissau.
Juyin mulkin Burkina na zuwa ne bayan wanda akayi a watan Agusta a kasar Mali, wanda kuma shine na biyu a kasar, bayan na kasar Guinea inda sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde.
Yayin da kungiyar ke lalubo hanyar dakile juyin mulki, sai aka samu irin wannan yunkuri na kifar da gwamnati da sojoji suka yi a kasar Guinea Bissau, matakin da ya kaiga rasa rayuka.
Ana saran taron na yau ya gabatar da matsayin sa akan halin da ake ciki a Burkina Faso sakamakon ganawar da tawagar ECOWAS tayi da shugabannin sojin kasar da kuma jaddada matsayin ta na adawa da juyin mulkin a yankin baki daya.
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU tare da ECOWAS duk sun dakatar da Burkina Faso bayan juyin mulkin da ya gudana a kasar.