Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ya Amince Da Murabus Na Wakilan Sadr.
Shugaban majalisar dokokin kasar Iraqi ya amince da murabus na gama gari wanda ‘yan majalisa masu goyon bayan Sayid Muktada Sadr suka yi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammed al-Halbousi yana fadar haka a shafinsa na twitter a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa “mun amince da murabus na dimbin yan majalisa masu goyin bayan babban malami shia Sayyid Muktada Assadr”
Kasar Iraqi dai ta kasa kafa gwamnati tun bayan zaben yan majalisar dokokin da aka gudanar a cikin watan Octoban da ya gabata. Inda gungun yan majalisa 73 masu goyon bayan malaman suka lashe zaben, wanda kuma su ne masu rinjaye a majalisar dokokin kasar.
RAED MORE : Abidjan – An Bude Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tattalin Arzikin Afirka.
Sai duk yawansu, hakan bai basu damar zaben wanda suka ga dama a matsayin firai minister ba, sai idan ya hada kai da wasu jam’iyyun. Sadr kuma ya ce ba zai hada kai da wata jam’iyya don kafa gwamnati ba.
READ MORE : Tehran Bunkasa Alakar Al’adu Tsakanin Iran Da Najeriya.
READ MORE : Birtaniya Ta Kame Shugaban Hukumar Leken Asirin Kasar Rwanda.
READ MORE : An sako wasu ‘yan kasar Siriya biyar daga hannun ‘yan ta’adda a arewacin Siriya.