Iran; ‘Yan Majalisar dokoki Sun Ce IAEA Da Shugabanta Sun Rasa Mutunci Saboda Nuna Bambanci.
‘Yan majalisar dokokin kasar Iran 260 sun bayyana cewa hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, da kuma shugaban hukumar sun rasa mutuncinsu bayan da suka amince da kudurin wanda yake zargin Iran da rashin bada hadin kai da ita. Har’ila yau da kuma ziyarar da shugaban hukumar Rafael Grossi ya kai HKI duk da cewa bata yarda da yarjejeniyar NPT ba kuma bata sanya hannu a kanta ba.
‘Yan majalisar sun kara da cewa wadannan halaye na hukumar da kuma shugabanta ya nuna cewa ta dauki bangare a ayyukanta, sannan ta sanya siyasa a cikin ayyukanta, na kwance damarar kasashe masu makaman nukliya a duniya.
A ranar laraban da ta gabata ce majalisar gwamnonin hukumar IAEA ta amince da daftarin kuduri wanda kasashen Amurka, Faransa, Jamus da kuma Burtaniya suka gabatar wanda yake zargin Iran da rashin bada hadin kai da hukumar.
READ MORE : PSG Ga Gab Da Kulla Kwantiragi Da Zidane Don Maye Gurbin Pochettino.
Wadannan kasashe hudu dai suna daga cikin kasashen da suka rattabawa yarjejeniyar JCPOA na shirin nukliyar kasar Iran a shekara ta 2015.
READ MORE : Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ya Amince Da Murabus Na Wakilan Sadr.