Senegal; An Yi Arangama Tsakanin ‘Yan Sanda Da ‘Yan Adawa.
Rahotanni daga Senegal na cewa akalla mutum biyu ne suka mutu sakamakon arangamar da akayi tsakanin ‘yan sanda da kuma ‘yan adawa a wasu sassan kasar da suka hada da Ziguinchor na Casamance.
Bayanai sun ce rikici ya barke tsakanin matasa da ‘yan sanda a ranar Juma’a a Dakar babban birnin kasar da kuma kudanci kasar.
Rikici dai tsakanin ‘yan adawa da masu mulki ya yi kamari a baya baya nan wata guda da rabi gabanin zaben ‘yan malasalisar dokokin kasar.
Kakakin jam’iyyar Pastef Ousseynou Ly ya ce an kama wasu ‘yan adawa uku, kana kuma jami’an tsaro sun hana jagoran ‘yan adawa Ousmane Sonko da kuma magajin brining Dakar fita gidajensu.
READ MORE : Bincike Bincike Na Dora Alhakin Kisan Abu Akleh Ga Isra’ila.
A Senegal dai ana fargabar samun tashin hankali tun bayan da hukumomi suka haramta wa ‘yan adawa gudanar da zanga-zanga da kuma soke jerin sunayen ‘yan takarar na adawa a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da aka yi a ranar 31 ga watan Yuli.
READ MORE : Abdullahian; Bai Kamata Kasashen Waje Su Yi Tasiri A Harkokin Tsaron Gabas Ta Tsakiya Ba.
READ MORE : Ra’isi; Ya Kamata Duniya Ta Fahimci Cewa Amurka Ba Abun Yarda Ba Ce.