Bincike Bincike Na Dora Alhakin Kisan Abu Akleh Ga Isra’ila.
Kafofin yada labarai na ci gaba da fitar da bayanai game da kisan ‘yar jaridar nan ta tashar talabijin ta Al Jazeera, Shireen Abu Akleh, wacce aka bindige har lahira a lokacin da take tsaka da aiki a yankin Jenin yayin samamen sojin Isra’ila.
Binciken baya-bayan nan shi ne na gidan talabijin na Al Jazeera, wanda ‘yar jaridar ke wa aiki, wanda a karon farko ya fito da hoton harsashin da ya kashe Shireen Abu Akleh, wani nau’in harsashi wanda mayakan Falasdinawa ba sa amfani da su.
Dama dai kafar yada labarai ta CNN ta Amurka, bisa da dogaro da wani bincike, ta ce an kashe Shireen Abu Akleh a wani hari da sojojin Isra’ila suka shirya.
Ita Jaridar Washington Post ta yi nuni da cewa da gangan wani sojan Isra’ila ya kashe ‘yar jaridar ta Aljazeera.
Saidai wadanan sakamakon binciken basu kai ga gamsar da gwamnatin Amurka ba kawo yanzu, a yayin da ya rage kasa da wata guda da ziyarar da ake sa ran shugaban kasar Joe Biden zai kai a yankin.
A yayin da aka cika kwanaki 40 da kisan ‘yar jaridar Shireen Abu Akleh, a yau Asabar ne ake wa ‘yar jaridar addu’o’i a wani coci da ke gabashin birnin Quds.