Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar da sanarwa dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Riyadh da Washington dangane da tafarkin kulla alaka tsakaninta da Isra’ila.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) – ABNA-ya habarta cewa: ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar da sanarwa dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Riyadh da Washington dangane da tafarkin sabunta huldar diblomasiyya tsakaninta da Isra’ila.
A cikin bayanin wannan ma’aikatar ya zo cewa: Dangane da tattaunawar da ake yi tsakanin Saudiyya da Amurka dangane da tafarkin zaman lafiya da dorewar sabunta hudlar akala tsakaninta da Isra’ila bias dogaro da abin da kakakin majalisar tsaron kasar Amurka ya fada dangane da hakan cewa muna jaddada matsayin Masarautar Saudiyya dangane da batun Palastinu da Bukatar ‘yan uwantaka na Falasdinu na halaccin hakkokinsu ya kasance kuma zai kasance mai dorewa.
Bisa rahoton da Kamfanin dillancin labaran Sama ta fitar da ke cewa, wannan sanarwar ta kara da cewa: Har ila yau Riyadh ta sanar da matsayarta kaitsaye ga gwamnatin Amurka da cewa: Saudiyya ba zata sabunta kulla huldar jakadancin difloma siyya tsakaninta da Isra’ila ba har sai an kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a kan iyakokin 1967 tare da zamowar gabashin birnin Kudus a matsayin babban birninta, kuma har sai haramtacciyar kasar Isra’ila ta dakatar da kai hare-harenta kan iyakar Zirin Gaza, kuma har sai dukkan sojojin mamaya na Isra’ila sun janye daga zirin Gaza kana.
Saudiyya ta ci gaba da cewa: Riyadh ta jaddada bukatar ta ga kasashen duniya – musamman ma – kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun, wadanda har yanzu ba su amince da kasar Falasdinu ba, ta na mai kira da cewa a gaggauta amincewa da kasar Falasdinu a kan iyakokin 1967 da Gabashin Kudus a matsayin kasar Falasdinu, domin al’ummar Palasdinu su samu hakkinsu da kuma samar da cikakken zaman lafiya da adalci ga kowa da kowa.
Sanarwar ta zo ne bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana a daren jiya Talata cewa, Saudiyya na da sha’awar daidaita dangantakarta da ‘yan mamaya, amma Yarima mai jiran gado na Saudiyya muhammad bin Salman ya bayyana karara cewa dole ne a kawo karshen yakin Gaza, kuma ya kamata a yi hakan a “tabbataccen tafarkin, abin dogaro kuma mai daure lokaci” don kafa kasar Falasdinu.
Source: ABNAHAUSA