Sarkin Kuwait Ya Amince Da Murabus Din Da Gwamnatin Kasar Ta yi.
Kamfanin dillancin laraban kasar Kuwait KUNA ya sanar cewa Takardar yin Murabus din gwamnati da Fira minister sheikh sabah Al Khalid Al-sabah ya mikawa sarkin kasar ta samu amincewa yarima mai jiran gado na kasar, kuma ya kafa wata doka da ta bawa majalisar ministocin ci gaba da rike rike mukami na wucin gad, sai dai dokar ba ta ayyan lokacin da za’a sake kafa wata sabuwar gwamnati ba.
An mika takardar yin murabus din ne tun a ranar 5 ga watan Aprilun bayan rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da kuma mjalisar dokin da hakan ya kawo cikas wajen aiwatar da wasu sauye –sauye a bangaren harkokin kudi a kasar.
An rantsar da sabuwar gwamnatin ne a watan Decembar shekarar da ta gabata,kuma ta 4 a acikin shekara biyu bayan wadda ta yi Murabus a watan Nuwambar da ya gabata,
Kasar Kuwait ta bawa majalisa karfin iko da yin tasiri sosai fiye da sauran takwarorin ta na tekun fasha, da suka hada da zartawar da kumtoshe wasa u dokokin, da kuma yin tambayoyi ga ministoci da mika bukatar nuna rashin yarda da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.