An shiga dare na biyu da fara kone kone a Sri Lanka.
An shiga rana ta biyu da fara ƙone-ƙonen gidaje da gine-gine a garin Negombo da ke kusa da babban birnin Sri Lanka wato Colombo.
Wani gungun ‘yan daba sun lalata wani wajen shaƙatawa mallakar dan tsohon firaministan kasar, Mahinda Rajapaksa.
A ranar Litinin, matsalar da tattalin arzikin kasar ke ciki ya kara harzuka al’ummar kasar musamman ma bayan da magoya bayan gwamnati suka kai wa masu zanga-zangar son Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya sauka hari.
Mutum takwas sun rasa rayukansu tun daga lokacin.
Kazalika an yi amanna akwai wasu 200 da suka samu raunuka a yayin gwabzawa.
An shafe makonni ana zanga-zanga a Sri Lanka, saboda matsalar rashin kudin da kasar ke fama da shi abin da ya janyo darajar kudin kasar ta fadi sannan kuma ake fama da karancin abinci da man fetir a kasar.
READ MORE : Barazanar Isra’ila Na kashe Jagororin Falasdinu Ba Zai Hana Ci Gaba Da Gwagarmaya Ba.
A daren ranar Litinin kadai, gungun ‘yan daban sun kona gidaje fiye da 50 na ‘yan siyasa.
READ MORE : Sarkin Kuwait Ya Amince Da Murabus Din Da Gwamnatin Kasar Ta yi.
READ MORE : Ziyarar Shugaban Kasar Siriya A Tehran Bude Wani Sabon Shafin Dangantaka Ne.