Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, zai ziyarci wasu kasashen yammacin Afirka daga karshen wannan mako domin bayyana irin illar da yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine ya yiwa nahiyar Afirka da wasu muhimman batutuwa.
Bayan ziyarar da ya kai zuwa Rasha da Ukraine a cikin makon da ya kare, Guterres zai isa Senegal da yammacin ranar Asabar don ziyarar aiki a ranakun 1 da 2 ga Mayu.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar zai kuma yi tattaki zuwa Nijar inda zai kasance har zuwa ranar 3 ga watan na Mayu, kafin ya kammala rangadinsa a Najeriya a ranakun 3 da 4 ga dai watan.
Bayan tattaunawa da shugabannin kasashen uku da zai ziyarta, Guteress zai kuma gana da wakilan kungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai.
A wani labarin na daban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana goyan bayan kungiyar kasashen Afirka ta AU wajen jagorancin sassanta rikicin kasar Libya, bayan ya amince da watsi da kungiyar da kasashen duniya suka yi wajen sasanta rikicin.
Guterres dake halartar taron kungiyar kasashen Afirka dake gudana a Addis Ababa yace ya fahimci fushin kungiyar, kuma ya zama wajibi a sanya ta cikin duk wani yunkuri.
Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa da zai karbi shugabancin kungiyar AU daga ranar litinin yace shugabancin sa zai mayar da hankali kan warware rikicin kasar Libya.
Shugabannin kungiyar kasashen Afirka sun koka kan yadda aka sanya su a gefe, a yunkurin da kasashen Duniya keyi wajen sassanta bangarorin dake rikici a Libya, cikin su harda Majalisar Dinkin Duniya da wasu kasashen Turai.
Kasar Libya ta fada cikin tashin hankali tun daga shekarar 2011 lokacin da kungiyar NATO ta goyi bayan boren da ya kawar da shugaba Muammar Ghadafi daga karagar mulki.
Yanzu haka kasar a rabe take tsakanin gwamnatin dake samun goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Yan Tawaye Janar Khalifa Haftar.