Cristiano Ronaldo mai shekaru 37 ne ya ci dukkannin kwallaye 3 a wasan da kungiyarsa, Manchester United ta lallasa Tottenham da ci 3 da 2 a daren Asabar, lamarin da ya sa har yanzu United ke da kwarin gwiwar kasancewa a cikin kungiyoyi 4 na saman teburin gasar Firimiyar Ingila.
Ana saura minti 10 a tashi wasa ne dan wasan na kasar Portugal ya saka wata kwallo da kai, wadda ita ce kwallonsa ta 807.
Bayan saka wannan kwallo a raga ce aka sauya Ronaldo, wanda magoya baya suka mike tsaye, su na masa jinjina a yayin da yake barin filin wasa.
Yanzu Ronaldo ya zarce wadannan ‘yan wasa a wajen yawan kwallaye: J. Bican 805, Romario 772, Pele 767 da Messi 759.
A wani labarin na daban An dakatar da cinikin kungiyar Chelsea kamar dai yada mammalakin wannan kungiya dan kasar Rasha Abramovich ya bukaci a yi a baya.Daukar wannan mataki daga gwamnatin Birtaniya na zuwa ne bayan da hukumomin suka dau wasu sabin takunkumai sanadiyyar yaki da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.
Tun bayan da Rasha ta kaddamar da wannan mamaya zuwa Ukraine, mammalakin wannan kungiya ta Chelsea duk da nuna damuwar sa a kai, Abramovich dan shekaru 55 babu sunan sa daga cikin mutanen da suka fuskanci wata barrazana daga kasashen Duniya.
Soke batun cinikin wannan kungiya ta Chelsea da gwamnatin Birtaniya ta yi na zuwa a wani lokaci da Rasha duk da zaman tattaunawa da aka soma,na saka attajirin Abramovich cikin wani yanayi marar kyau,duk da cewa gwamnatin Birtaniya ta sanar da daukar wasu jerryn matakai na yin sassauci ga kungiyar ta Chelsea tare da bata damar ci gaba da taka tamola a fagen gasar ta Frimiya ta Ingial.
A karshe yanzu kam kungiyar ta Chelsea na fatan shiga tattaunawa da hukumomin Birtaniya don ganin an cimma mafita a kan wannan matsalla.