Rahotanni daga falasdinu sun tabbatar da cewa an samu barkewar rikici tsakanin falasdinawa da yahudawa ‘yan share wuri zanuna a unguwar sheikh jarrah dake kusa da masallachin al’aqsa dake kasar falasdinu.
Labarai sun ishe mu dai cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wani dan majalisar haramtacciyar kasar isra’la daya bude ofishi a unguwar wacce ta falasdinawa ce, hakan ya jawo rikici da cece kuce amma an gano wani bidiyo inda yahudawan haramtacciyar kasar isra’ela suke jifan falasdinawa yayin da jam’an tsaron haramtacciyar kasar isra’ela ke abama yahudawan tsaro.
Dan majalisar na haramtacciyar kasar isra’ela Ben Gvir’s ya bayyana cewa zai cigaba da zama a unguwar falasdinawan ta sheikh jarrah duk da rashin dacewar hakan domin a cewar sa dole ne a bama yahudawan isra’ela masu halartar unguwar tsaro.
Daren daya gabata dai yahudawan isra’ila sun afka unguwar falasdinawan ta sheikh jarrah inda suka tsorata falasdinawa da dama gami da kokarin aiwatar da ayyukan ta’addanci tare da kokarin fitar da wasu daga cikin falasdinawa daga gidajen su.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar yahudawan isra’ilan wadanda suka bisa tsaron sojojin isra’ila sun fada unguwar falasdinawan ta sheikh jarrah inda suka tada rikici kuma suna jefa duwatsu cikin gidajen falasdinawan inda kuma suka lalata ababen hawan wasu daga cikin falasdinawan abinda ke zaman musgunawa ga larabawan falasdinu mazauna unguwar ta sheikh jarrah.
Tsawon shekaru dai mazauna unguwar sheikh jarrah ke fuskantar musgunawa daga yahudawan wadanda ke fadowa unguwar su tada rikici kuma su hana kowa zaman lafiya tare da hakan kuma suna samun goyon baya daga sojojin haramtacciyar kasar isra’eilan wadanda tare suke zuwa dasu.
Manyan kasashen larabawa dai sunyi shiru dangane da bakin zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ila ke aiwatarwa a kan musulmi larabawa a tsawon wadannan shekaru.
Majiyar mu tabbatar mana da crewa zuwa yanzu dai falasdinawa basu da mataimakin daya wuce kasar Iran.