Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da shirin kafa manya-manyan sansanonin sojinta a yankin yammacin kasar don martini ga NATO kan dauki dai-dai da ta ke yiwa kasashen gabashin Turai, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da wasu Sojin Ukraine kusan dubu 2 suka mika wuya ga Moscow.
Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce kafa sabbin sansanonin Soji wajibi ne don dakile barazanar da kasar ke fuskanta daga kungiyar da ta kira babbar makiyiyarta wato NATO.
A wata sanarwar kai tsaye da ministan tsaron Sergei Shoigu ya yi ta gidan talabijin, ya bayyana cewa zuwa nan da karshen shekara za su samar da sansanonin Soji akalla 12 a yammacin kasar, wadanda za a wadata da manyan makaman kare kai.
Bayan matakin shugaba Vladimir Putin na aikewa da dakaru Ukraine a ranar 24 ga watan fabarairun da ya gabata lamarin da ya yamutsa zaman lafiyar duniya, matakin ya sanya kasashen Finland da Sweden da suka shafe shekaru a matsayin ‘yan ba ruwanmu neman izinin shiga NATO.
Dai dai lokacin da yakin na Rasha da Ukraine ke ci gaba da tsananta, zuwa yau juma’a akalla Sojin Ukraine 1908 suka mika wuya bayan da ma’aikatar tsaron kasar ta umarce su da su ajje makamansu don neman maslaha da Rasha.
Wasu bayanai sun ce gwamnatin Ukraine na son musayar dubunnan sojojin da Rasha ta akme mata da fursunonin Moscow da yanzu haka ke hannunta.
A wani labarin na daban kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha a jawabinsa yayin bikin tunawa da nasarar tarayyar soviet kan dakarun Nazi a yakin duniya na 2, ya ce dakarunsa yanzu haka na yaki ne a Ukraine don kare martabar kasarsu, ya na mai cewa dukkanin ran soja guda da Moscow ta rasa a yakin ya na sosa ran kasar baki daya.
Acewar Putin cikin jawabin nasa gaban dubunnan dakarun Soji da fararen hular da suka yi dandazo a dandalin taron, dole ne su yi yaki don kare martabar Rasha da kuma katange ta daga mamayar abokanan gaba ciki har da kungiyar NATO.
Shugaba Putin ya sha alwashin bayar da cikakkiyar kulawa ga daukacin iyalin dakarun soji da ‘yan sa kai da suka rasa rayukansu wajen kare kasarsu.
Putin lokacin da ya ke gaisawa da wasu daga cikin Sojojin da suka gwabza da dakarun nazi a yakin duniya na biyu.
Putin lokacin da ya ke gaisawa da wasu daga cikin Sojojin da suka gwabza da dakarun nazi a yakin duniya na biyu. via REUTERS – SPUTNIK
Dubban ‘yan kasar Rasha ne dai suka halarci bikin faretin ranar ‘yancin da aka gudanar a birnin Moscow domin tuna shekaru 77 da kawo karshen yakin duniya na 2 wanda kuma samun nasara akan sojojin Nazi.
Rasha na gudanar da irin wadannan bukukuwa da suka shafi baje kolin makamai da kuma nuna karfin sojin ta ne kowacce shekara a ranar 9 ga watan Mayu, yayinda a wannan karon bikin ya zo lokacin da kasar ke yaki da makwabciyar ta Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin rike da hoton mahaifinsa Vladimir Spiridonovich Putin wanda gwarzo ne a yakin duniya na 2.
Shugaba Vladimir Putin rike da hoton mahaifinsa Vladimir Spiridonovich Putin wanda gwarzo ne a yakin duniya na 2. REUTERS – MAXIM SHEMETOV
Shugaba Vladimir Putin wanda ya dauki hotan mahaifin sa ya rike lokacin faretin, ya bayyana cewar dakarun kasar da ke yaki a Ukraine suna fada domin kare kasar su ce.