Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta yi amfani da sabon makami mai linzami mai matsanancin gudu a karon farko wajen lalata rumbunan makaman Ukraine.
Rasha ba ta taba yarda cewa t yi amfani da wannan makami mai linzami ba, kuma kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa wannan ne karo na farko da ta yi amfani da makamin da aka wa lakabi da Kinzhal a yammacin Ukraine.
Makami mai linzami na Kinzhal mai dankaren gudu, wanda aka kwatanta da gudun sauti ninki 10, ya lalata dimbim rumbunan makamai masu dauke da makamai masu linzami da alburushan harbo jiragen sama a kauyen Deliatyn, a yankin Ivano-Frankivsk.
Sai dai wani kakakin ma’ikatar tsaron Rasha ya kauce wa yin karin bayani a lokacin da kamfanin dillancin labaran Faransa ya tuntube shi.
Putin ya yi bayani a kan Kinzhal
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana makamin Kinzhal, mai linzami a matsayin makmin da ya dace da aikin da suke yi, wanda gudunsa ya ninka na sauti sau 10, kuma babu na’urar da za ta iya kakkabo shi.
Makamin na Kinzhal na daya daga cikin makaman da Putin ya baje kolinsu a yayin da ya gabatar da jawabi kan halin da kasar ke ciki a shekarar 2018.
A wani labarin na daban Kotun Duniya da ke birnin Hague a Holland ta umarci Rasha ta gaggauta dakatar da mamayar da ta ke yi wa Ukraine, dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ita ma a bangare guda ke sake mika rokonta ga Rasha wajen ganin an kawo karshen yakin tare da warware rikicin ta lumana.
Hukuncin kotun na ICJ da ke biyo bayan karar da Ukraine ta shigar ranar 27 ga watan Fabarairu kwanaki 3 bayan mamayar da Rasha ta fara yi mata ya umarci Moscow ta janye dakarunta daga sassan Kiev cikin sauri, a kokarin tabbatar da zaman lafiya tsakaninta da makwabciyartata.
Hukuncin kotun wanda babu tabbacin ko Rasha za ta mutunta shi, na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun kasar ke ci gaba da yiwa manyan biranen Ukraine kawanya, hare-haren hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ke cewa zuwa yanzu ya hallaka fararen hula dubu 1 da 834.
Tuni Ukraine ta bayyana hukuncin na ICJ da gagarumar nasara yayinda ta sha alwashin ci gaba da matsa kaimi har zuwa lokacin da Rashan za ta janye tare da dawowar zaman lafiya a sassan Kiev da kewaye.
Majalisar dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu fararen hula fiye da miliyan 3 ne suka yi kaura daga yankunan da Moscow ta yiwa mamaya don tsira da rayukansu daga hare-haren Sojin.
Mai shari’a Joan Donoghue da ya jagoranci zaman shari’ar na yammacin jiya laraba, ya bayyana kotun ta ICJ a matsayin fadar tabbatar da adalci yana mai nuna damuwa da yadda Rasha ke amfani da karfin Soji a rikicin maimakon warware shi ta ruwan sanyi.
Bayanai sun ce ICJ ta zartas da hukuncin ne ba tare da halartar wakilcin Rasha a zaman shari’ar ba.
Cikin hujjojin da Ukraine ta kafa wajen shigar da karar gaban kotu shi ne zargin Rasha da kokarin kisan kare dangi kwatankwacin na shekarar 1948 batun da tuni Moscow ta musanta yayin zaman sauraren shari’ar na ranakun 7 da 8 ga watan da muke ciki bisa cewa babu hujjar da ke tabbatar da zargin.
Rasha dai na ci gaba da nanata cewa, matakinta na amfani da Soji a Ukraine kokari na kare kanta daga barazanar tsaron da ta ke fuskanta daga makiyanta da kungiyar tsaro ta NATO.