Rasha ta sallami jami’an Diflomasiyyar Jamus guda 2 a wani yanayi da ke matsayin martanin kan hukuncin da wata kotun Berlin ta yi da ya tabbatar da Moscow a matsayin wadda ta dauki nauyin kashe tsohon babban kwamandan Chechenia.
Tuni dai gwamnatin Rasha ta aikewa da babban jami’in diflomasiyyar Jamus din da ke kasar takaradar da ke umartar sa da ya bar kasar ba tare da wani bata lokaci ba.
Baya ga haka kuma kasar ta ce zata baiwa al’ummar ta damar gabatar da zanga-zanga don nuna fushin su kan hukuncin da kotun ta zartas wanda take ganin an yi amfani da zallar son zuciya.
Tun da fari dai Russian tace kutugwilar siyasace kawai Jamus take son kulla mata, dalili kenan da ya sanya ta yanke wannan hukunci mai cike da son zuciya.
Tuni dai masana harkokin diplomasiyya ke ganin cewa daukar wannan mataki zai kara tsamin dangantaka a tsakanin kasashen biyu, tare kuma da sake tunzura rashin jituwar dake tsakanin sauran kasashen yamma da Russia kan batun Ukraine.
A wani labarin na daban a wani mataki na wucin gadi Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana dakatar da horon da take bai wa dakarun sojin kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sakamakon aikin tsaron da sojojin hayar kamfanin Wagner na kasar Rasha ke yi a kasar, kamar yadda tawagar kungiyar Tarayyar Turan dake Bangui ta sanar.
Kamar yadda babban komandan dakarun Turai a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Janar Jacques Langlade de Montgros, ya sanar wa kamfanin dillancin labaran Faransa.
Janar Montgros ya ci gaba da cewa, sojojin hayar na bai wa dakarun kasar ta JAT horo, da kuma da ayukan tsaro ne ya sa kungiyar ta turai ta dakatar da nata horon da take baiwa sojojin kasar na wucin gadi
sai dai kungiyar ta turai ta ce, horon da take baiwa rundunar sojin na JAT zai iya ci gaba, matsawar ta samu tabbacin cewa, sojojin JAT da ta horar ba za su yi aiki tare da sojojin sa kai na Wagner”ba.
Yanzu haka dai tuni kimanin masu bada horon kungiyar tarayyar turan 70 ne suka koma kasashensu na asali.