Rasha Da Ukraine Sun Koma Bakin Tattaunawar Sulhu A Karo Na Uku.
Wakilan kasashen Rasha da Ukraine sun koma bakin tattaunawar neman sulhu yau Litini da ake akan iyakar Belarus da Poland.
Wannan ita ce tattaunawa ta uku tsakanin bangarorin biyu tun soma yakin na Ukraine, wanda ya shiga kwana na 12 a yau.
Kafin hakan dai kasar Ukraine ta ki amincewa da tayin Rasha na kwashe fararen hula a yankunan da ake barin wuta.
Gwamnatin ta Ukraine, ta ce bata amince da shawarar da Moscow ta gabatar, na samar da hanyoyin jin kai domin fitar da fararen hula zuwa Belarus da kuma Rasha.