Ralf Rangnick ya ce yunkurawar Manchester United ta yi, inda ta jaddada nasarar da ta samu tun da farko a wasanta da Leeds united har ta lallasa ta 4-2 a jiya Lahadi ita ce amsa ma fi dacewa ga cece- kucen da ake na cewa rikici ya tashi a tsakanin ‘yan wasan kungiyar.
Abin da ya fi ci wa Ragnick tuwo a kwarya tun da ya fara aikin wucin gadi a matsayin kocin Manchester United shine gaza kare nasarar da yake fara samu a wasa, kuma sai da aka kusan yin haka, bayan da United ta saka wa Leeds kwallaye 2, amma suka farke.
Amma a wannan karon, ‘yan wasan united sun yunkuro sun kare martabarsu, inda Fred da Anthony Elanga suka saka kwallo daya kowanne.
Shi ma kaftin Harry Mcguire ya mayar da martini da sukar da ake mai ta wajen saka kwallon United ta farko a wasan a cikin minti na 34.
A wani labarin na daban Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya yi ikirarin cewa zai zama abin kunya idan har kungiyarsa ta gaza kammala gasar firimiyar bana a sahun ‘yan ukun saman teburi dai dai lokacin da mai horarwa Ralf Rangnick ke kokarin dawo da tawagar turbar nasara biyo bayan rashin abin kirki a wasanni da dama da ya kai ga sauya manaja.
Sai dai Ronaldo na Portugal mai shekarau 34 wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Ballon d’Or har sau 5 ya ce dolensu ne matsayin ‘yan wasan kungiyar su sauya tunani tare da jajircewa don ganin basu yi abin kunya a karshen kaka ba.
Kalaman na Ronaldo na zuwa bayan shan kayen da United ta yi a hannun Wolves da ya janyowa kungiyar caccaka inda dan wasan ke cewa a zuciyarsa ya na ganin tabbas za su iya kammala firimiya matsayin na 2 ko na 3 ko da basu iya dage kofin a wannan karon ba.
Acewar Ronaldo bai zo firimiya don karkare kaka a matsayin na 6 ko na bakwai ba fatansa shi ne sake dage kofin firimiya tare da tsohuwar kungiyar tasa kuma har zuwa yanzu bai karaya ba.