Ra’isi Muna Alfahari Ne Da Al’ummarmu A Duk Inda Suke Wajen Samar Da Ci gaba.
Shugaban Iran, Ebrahim Ra’asi, ya bayyana cewa kasar na alfahari da tafarkin da take a kansa, wanda ke ci gaba da haskaka a duniya.
M. Ra’asi, ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatar na zagayowar shekaru 43 na nasarar juyin juya halin musulinci a kasar.
‘’ Ya kara da cewa mun dogara da al’ummarmu abun kauna a duk inda su ke a duniya, wajen farfado da tattalin arziki da kuma ci gaba, bamu taba dogoro da wani Vienna ba ko New York’’
Ba kuma zamu amincewa ba da danniyya ko kuma watsi da yancinmu, inji shugaba Ra’asin.
A jiya Juma’a ne aka gudanar da bukukuwan cika shekaru 43 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar ta Iran.
Kamar kowace shekara, 11 ga watan Fabarairu wadda ta yi daidai da ranar 22 ga watan Bahman a kalandar Iraniyawa, al’ummar kasar na murnar zagayowar wannan rana wacce ta samu karkashin jagorancin Ayatollah Imam Khomeini wanda ya asasa jamhuriyar musulinci ta Iran, bayan ya dawo kasar daga gudun hijira a faransa, bayan boren jam’ar kasar da ya kai ga faduwar mulkin sarki Shah a waccen lokacin.