Shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi i ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta bar teburin tattaunawa da kungiyar P4+1 kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 ba, kamar yadda kuma ba za ta dora da hakan ba a kan sauran harkokin na ci gaba.
“Ba za mu danganta ci gaban kasarmu da warware matsalolin da suke da alaka da yarjejeniyar nukiliya ba, inji Ibrahim Ra’isi a lokacin da yake jawabi a yammacin jiya a lardin Kerman da ke kudu maso gabashin kasar Iran.
Ra’isi ya ce, ci gaban Iran da tattalin arzikinta ba za su taba komawa baya ba saboda nasara ko rashin nasarar tattaunawar da ake yi.
Iran ta bayyana cewa Amurka c eke kawo dukkanin tsaikon da ake samu a tattaunawar, kasancewar har yanzu ba a warware wasu muhimman batutuwa da suka hada da kawar da duk wani takunkumin da aka kakaba mata bayan yarjejeniyar 2015 ba, da kuma kin bayar da lamuni daga bangaren Amurka kan cewa ba za ta sake ficewa daga yarjejeniyar ba kamar yadda ta yi a baya.
Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya fada a watan da ya gabata cewa dole ne Iran ta samu fa’idar tattalin arziki daga yarjejeniyar 2015, saboda haka dole ne ta samu lamuni mai karfi kan hakan kafin ta amince da duk wasu shawarwari da za a gabatar mata.
Iran dai ta koma teburin tattaunawa da manyan kasashen turai ne bayan tsagaita tattaunawar da akayi sakamakon wadansu matsaloli daga bangaren kasashen turai din.
Yarjejeniyar JCPOA wacce aka kulla da nufin samar da matsaya tsakanin kasashen turai da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dai amurka ce ta sa kafa ta fice daga yarjejeniyar abinda ya rusa yarjejeniyar wacce yanzu manyan kasashen ke kokarin farfado da ita.
Source: ABNA