Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi barazanar katse ci gaba da kasancewar Ukraine a matsayin yantatar kasa, a yayin da mamayar da ya yi wa kasar ke ci gaba da gamuwa da turjiya, kuma tattalin arzikin kasarsa ke dada dankwafewa sakamakon takunkumai masu gauni.
Rasha ta ci gaba da kai hare hare Ukraine, amma shugaba Zelensky wanda ke turjewa ya ce dakarunsa na mayar da zazzafan martani a yankin Kharkiv, birni na biyu mafi girma a kasar, kuma su ma maharan na dandana asarar da ko a mafarki ba su taba gani ba.
Shi ma ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba cewa yake, jini na kwarara daga Ukraine, amma sam, ba ta fadi ba, yana mai cewa asirin sojin Rasha da ke da karfin gaske ya tonu.
A wani labarin na daban kuma Rahotanni daga Jihar Neja a Najeriya sun ce an sake samun fashewar bam a yankin Galadima-Kogo da ke karamar hukumar Shiroro.
Wasu majiyoyi sun ce fashewar ta auku ne da kusan karfe 7 na, yammacin ranar Juma’a.
Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai babu cikakken bayani kan adadin mutanen da fashewar bam din ta ritsa da su a yankin na Galadima-Kogo.