Shugaba Vladimir Putin na Rasha a jawabinsa yayin bikin tunawa da nasarar tarayyar soviet kan dakarun Nazi a yakin duniya na 2, ya ce dakarunsa yanzu haka na yaki ne a Ukraine don kare martabar kasarsu, ya na mai cewa dukkanin ran soja guda da Moscow ta rasa a yakin ya na sosa ran kasar baki daya.
A cewar shugaban cikin jawabin nasa gaban dubunnan dakarun Soji da fararen hular da suka yi dandazo a dandalin taron, dole ne su yi yaki don kare martabar Rasha da kuma katange ta daga mamayar abokanan gaba ciki har da kungiyar NATO.
Shugaba Putin ya sha alwashin bayar da cikakkiyar kulawa ga daukacin iyalin dakarun soji da ‘yan sa kai da suka rasa rayukansu wajen kare kasar su.
Putin lokacin da ya ke gaisawa da wasu daga cikin Sojojin da suka gwabza da dakarun nazi a yakin duniya na biyu.
Putin lokacin da ya ke gaisawa da wasu daga cikin Sojojin da suka gwabza da dakarun nazi a yakin duniya na biyu. via REUTERS – SPUTNIK
Dubban ‘yan kasar Rasha ne dai suka halarci bikin faretin ranar ‘yancin da aka gudanar a birnin Moscow domin tuna shekaru 77 da kawo karshen yakin duniya na 2 wanda kuma samun nasara akan sojojin Nazi.
Rasha na gudanar da irin wadannan bukukuwa da suka shafi baje kolin makamai da kuma nuna karfin sojin ta ne kowacce shekara a ranar 9 ga watan Mayu, yayinda a wannan karon bikin ya zo lokacin da kasar ke yaki da makwabciyar ta Ukraine.
Shugaba Vladimir Putin rike da hoton mahaifinsa Vladimir Spiridonovich Putin wanda gwarzo ne a yakin duniya na 2.
Shugaba Vladimir Putin rike da hoton mahaifinsa Vladimir Spiridonovich Putin wanda gwarzo ne a yakin duniya na 2. REUTERS – MAXIM SHEMETOV
Shugaba Vladimir Putin wanda ya dauki hotan mahaifin sa ya rike lokacin faretin, ya bayyana cewar dakarun kasar da ke yaki a Ukraine suna fada domin kare kasar su ce.