Kungiyar PSG na kasar Faransa na gab da cimma yarjejeniya da Zinedine Zidane a matsayin sabon cocinta da zai maye gurbin Mauricio Pochettino.
A cewar gidan radiyon Europe 1, kungiyar na kan tattaunawa domin tsohon kocin na Real Madrid mai shekaru 49 ya koma PSG kafin sabuwar kakar wasanni.
Da Kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntubi majiyar PSG, ta ki amincewa ko ta musanta rahotannin.
Kwantaragin Pochettino Bai Kare Ba
Pochettino dai yana da sauran shekara guda kan kwantiraginsa da PSG kuma ya jagoranci kungiyar da Qatar ke marawa baya samun nasara a gasar Ligue 1 a kakar da aka Karkare, to amma Real Madrid ta fitar da su daga gasar zakarun Turai a zagaye na ‘yan 16
Burin lashe Gasar Zakarun Turai
Masu kulob din na Qatar na da burin lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Turai kuma Zidane ya jagoranci kungiyar ta Spain ta lashe kofin kaka uku a jere tsakanin 2016 da 2018.
Tsohon dan wasan da ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 1998, Zidane ya lashe gasar zakarun Turai a lokacin da yake dan wasa a Real a 2002.
A wani labarin na daban zinedine Zidane ba zai horar da wata kungiya a wani lokaci na kusa ba saboda zai jinkirta har sai an samu gurbi a babbar tawagar kwallon kafar kasar Faransa, a cewar jaridar Libertad Digital.
Mai horar da tawagar kasar Faransar, Didier Deschamps ya ce ba shi da niyyar barin tawagar Faransa a wani lokaci a nan kusa, sabida haka Zidane zai yi zaman dakon lokacin da dan talikin zai yi hannun riga da tawagar.