An tabbatar da tsohon dan wasan baya na Liverpool Rigobert Song a matsayin sabon kocin Kamaru bisa umarnin shugaban kasar Paul Biya.
Song shi ne dan wasan da ya fi taka leda a kasar, inda ya buga wa kungiyar Indomitable Lions wasanni 137.Sanarwar ta ce Kamaru na bukatar “sake farfadowa a harkokin wasanninin kwallon kafa”.
Umurnin shugaban kasa
Ministan wasanni na Kamaru Narcisse Mouelle Kombi ya ce “A bisa umarni daga shugaban kasa mista paul biyar, an maye gurbin kocin kungiyar kwallon kafa ta maza, Mista Antonio Conceicao da Rigobert Song.”
“An gayyaci hukumar kwallon kafa ta Kamaru (Fecafoot) da ta dauki matakan da suka dace don aiwatar da umarni cikin sauri da kuma jituwa.”
FIFA
Sabon nadin ya haifar da cece-kuce tare da bada mamaki saboda dokokin Fifa sun bukaci kowace kungiya ta kasance mai zaman kanta tare da kaucewa duk wani katsalandan na siyasa.
Conceicao ya jagoranci Kamaru zuwa wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya kuma za su kara da Algeria a wasan daf da na karshe a watan Maris domin samun gurbi a Qatar 2022.
Song, wanda kuma ya buga wa West Ham ta Ingila wasa, kuma ya yi wasanni a Faransa da Italiya da Jamus da kuma Turkiyya a lokacin da yake buga wasa, ya kuma taka leda a gasar cin kofin duniya har sau hudu kuma ya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara ta 2000 da 2002.
A baya-bayan nan shi ne kocin tawagar ‘yan kasa da shekara 21 ta Kamaru.