A duk shekara, hukumomin kasar Saudiya na bullo da sabbin tsare-tsare don inganta jin dadin Alhazai da kuma yadda ake gudanar da aikin hajjin.
A shekarun baya an fuskanci rushe -rushe domin fadada wurare ibada masu tsarki inda Alhazai musamman ke yin cincirindo domin gudanar da ayyukan ibada.
Rashin issashen wuri ya haifar da mastaloli da dama a shekarun baya inda har aka kai ga rasa rayukan mutane da dama.
A wannan shekarar Hukumar Saudi ta bullo da katin tantance mai cikakken izinin kasancewa a wurare masu tsari da ake gudanar da aikin hajji. Katin da aka lakaba wa suna NUSUK ya zama wa wasu mahajjata alakakai, musamman ganin an samu jinkiri daga hukumar Alhazai na ba wasu Alhazai wannan katin, musamman lokacin da aka shigo garin Makkah.
Jami’an tsaron Saudiya sun yi ta kama wadanda ke zirga-zirga ba tare da makale da katin NUSUK a wuyarsu ba. Shiga masallacin harami ya gagari Alhazan da basu da katin NUSUK.
Wannan ya sa hukumar Alhazai ta NAHCON ta kara kaimi wajen ganin ta ba kowa katinsa na NUSUK a kan lokaci.
A bayaninsa na cikakken dalilin bullo da katin NUSUK, wani jami’n tsaro na kasar Saudiya wanda ya nemi mu sakaya sunansa saboda bashi da ikon yin magana da ‘yan jarida, ya ce, a shekarun baya bata gari na shigowa cikin tawagar Alhazai inda suke sace-sace musamman a yayin zaman Muna, Arafat da Muzdalifah, sannan kuma hakan zai taimaka wajen takaita hankoron wadanda basu da izinin gudanar da aikin Hajji shiga wurare masu tsarki inda haka yakan haifar da cunkoso, ga duk wanda ya samu gudanar da aikin hajjin bana zai bayyana maka yadda katin NUSUK ta nastar da shi.
Wannan tsari na NUSUK ya taimaka wajen samun cikakken adadin wadanda suka shigo Saudiya domin aikin hajji da kuma kididdigar daga inda suka shigo. Ma’aikatar aikin Hajji da Umara ta ce, alhazai 1,833,164 suka gudanar da aikin hajjin bana daga sassan duniya sun kuma shigo ne ta hanyoyi daban daban.
Wani abu kuma da ya dauki hankalin duniya gaba daya game da aikin hajjin bana, shi ne irin tsananin zafin ranar da aka yi a ranakun jifar jamra, wanda sai ta kai da hukumar kasar Saudiya, a ta bakin Ministan Umara Hajji Abdulfattah bin Suka bayar da umarnin a dakatar da tafiya jamrat na tsawon awa 5, aka kuma umarci Alhazai su lizimci sha ruwa a kai-kai su kuma guji gararamba a cikin ranar ba tare da wani dalili ba.
Hukumomi su da tabbatar da mutuwar mutum 20 yawancin su daga kasashe yankin nahiyar Asiya.
DUBA NAN: Zafi Yayi Sanadin Mutuwar Fiye Da 900 A Hajjin Bana
Duk an kammala aikin Hajjn 2024 hasashe ya nuna cewa, za a ci gaba da fuskantar karin zafin rana inda ake ganin zai iya kaiwa 50 zuwa 60 a ma’aunin zafi.