Nijar Ta Haramta Zangar zangar Kin Jinin Sojojin Faransa Da Tsadar Rayuwa.
Hukumomi a birnin Yamai, na jamhuriyar Nijar, sun haramta zanga zangar da gamayar wasu kungiyoyin fara hula suka shirya gudanarwa a ranar Larabar nan game da matakin kara kudin man Diezel, da tsadar rayuwa da kuma kin jinin sojojin faransa a kasar.
Wata sanarwa da hukumomin birnin Yamai suka fitar, ta ce an haramta zanga zangar bisa dalilai na tsaro, da fargabar samun ‘yan kuste da kuam tarbarbarewar al’amuran jama’a.
Kawancen da ake wa lakabi da M62, da aka kaddamar a ranar 3 ga watan Agustan nan, ya kunshi kungiyoyin fara hula kimanin 15, ya kira zanga zanga da gangami ne a duk fadin kasar domin tabbatar da adalci ga jama’a.
READ MORE : Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamai Masu Linzami.
Tuni dai kawacen ya kalubalanci matakin gaban shari’a, akamr shugabansa Mal. Abdoulaye Seydou, ya fada a wani taron manema labarai.
READ MORE : Eric Trump; Muna da faifan binciken da jami’an FBI suka yi a gidan Mare Lago.
READ MORE : EU Ta Fara Nazarin Ra’ayin Iran Dangane Da Farfado Yarjeniyar JCPOA.
READ MORE : Kasar Kuwait Ta Nada Sabon Jakadanta Na Farko A Kasar Iran Bayan Shekaru Shida.