Nijar Da EU Sun Cimma Sabuwar Yarjejeniyar Yaki Da Safarar Bakin Haure.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da kungiyar tarayyar turai sun cimma wata sabuwar yarjejeniyar yaki da safarar mutane.
A cewar ministan cikin gida na Nijar, Hamadou Adamou Souley, wannan sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tsare iyakoki, da bakin haure da kuma kyautata rayuwar kowa da kowa.
Abu mai mahimmanci shi ne yanzu tabbatar da sabin shirye shirye da kwamishinan kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin cikin gida ya sanar yayin ziyararsa a Agadas, da suka hada da tsare tsare na ci gaban tattalin arziki wanda zai baiwa masu dogoro da ayyukan da suka jibanci bakin hauren aikin yi, inji ministan cikin gidan kasar ta Nijar.
Tun a cikin shekarar 2015 ne gwamnatin Nijar da kungiyar ta EU suka cimm yarjejeniyar mai manufar yaki da safarar bakin haure ba bisa ka’ida ba.
READ MORE : Iran Ta Kaddamar Da Sabon Sashen Ruwa Na Jiragai Marar Matuka.
Tun daga sherarar 2017 masu safara mutane 700 aka cafke a kasar dake zaman wata hanya ta baki haure dake son shiga turai.
READ MORE : Marcus: Saudiyya Bata Damu Da Halin Da Falasdinawa Suke Ciki Ba.
READ MORE : Kashshogi: Shugban Amurka Ya Tuhumi Muhammad Bin Salman Na Saudiyya.