Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine ba, biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.
Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba da hare hare a fadin kasar.
NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane, ta dau wannan mataki ne duk da magiyar da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen kasarsa.
Ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman taimako.