Gwamnatin Najeriya ta yi tir da rahotanni akan yadda ake nunawa ‘yan Afirka wariyar jinsi cikin su har da ‘yan Najeriya da ke kokarin tserewa daga Ukraine zuwa kasar Poland sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Kiev.
Garba Shehu ya ce wani faifan bidiyon da ake ta yadawa ta kafar sada zumunta ya nuna yadda aka tilastawa wata mata ‘yar Najeriya da diyarta tashi daga kujerar jirgi domin bai wa wata ‘yar Ukraine ta zauna.
Sanarwar ta ce sun kuma samu labarin yadda jami’an kasar Poland ke hana ‘yan Najeriya tsallakawa kasar su daga Ukraine.
Shehu ya ce dole ne jami’an tsaro da na shigi da fice su fuskanci mutane fiye da yadda su ke tunani a irin wannan lokaci, saboda haka ya dace a mutunta kowanne mutum guda daga cikin su ba tare da la’akari da launin fatar jikin sa ko kuma inda ya fito ba.
Sai dai a nata bangare, Jakadiyar Poland a Najeriya Joanna Tarnawska ta yi watsi da zargin nuna banbancin, inda ta ce suna bai wa bakin kulawa ba tare da nuna banbanci ba.
Tarnawska ya tabbatar da cewar yanzu haka ‘yan Najeriya da dama sun tsallaka iyakar Ukraine zuwa cikin Poland domin samun mafaka.
Jakadiyar ta ce ‘yan Najeriyar da suka tsallaka iyaka na da kwanaki 15 su bar kasar ko kuma suyi wani shiri na musamman.