Najeriya ta haramta wa ‘yan kasarta zuwa Ukraine domin yakar Rasha.
Najeriya ta ce ba za ta ƙyale ‘yan kasarta su shiga cikin mayakan da ke yaki da Rasha a kasar Ukraine ba.
Wannan ya biyo bayan wasu rahotanni da ke cewa an fara yi wa ‘yan kasar ‘yan sa kai rijista domin su taimaka wa sojojin Ukraine a mamayar da Rasha ke yi wa kasar.
Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta ce ofishin jakadanci Ukraine da ke kasar ya musanta taka wata rawa a wannan abin takaicin.
Sai dai ofishin jakadancin ya tabbatar cewa wasu ‘yan Najeriya sun sanar da shi cewa a shirye suke a yi wannan yakin da su.
Ofishin jakadancin ya kuma nisanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya bukaci dukkan dan Najeriyar da ke son shiga yakin da ya biya dalar Amurka 1,000 a matsayin kudin tikitin jirgin sama da na biza.
Wannan matakin na Najeriya na zuwa ne bayan kwana daya da kasar Senega ta gargadi ‘yan kasarta masu sha’awar tafiya Ukraine da su guji daukan wannan matakin.
Ta umarci jakadan kasar Ukraine da ya sauke wasu bayanai da ofishinsa ya wallafa a Facebook yana kira ga ‘yan Senegal su yi rajista domin a tafi da su can su yi yaki.