Najeriya ta amince da bukatar hana baki ‘Yan kasashen waje sayen amfanin gona kai tsaye daga manoma ko kuma amfani da wakilansu, a wani yunkuri na bunkasa harkokin kasuwanci a cikin gida.
Adebayo ya ce sakamakon amincewa da wannan shirin, ‘Yan kasuwan cikin gida ne kawai da ke da lasisi ke iya cinikin amfanin gonaki kai tsaye daga manoma domin sayarwa baki ‘Yan kasashen waje.
Ministan ya ce wannan mataki zai toshe kofar cutar manoman da bakin keyi wajen karbe amfanin gonakin su da ‘Yan kudi kadan.
A wani labarin na daban Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce jami’an tsaro a gabashin kasar Chadi sun kashe masu zanga-zanga akalla 13, ciki har da wani yaro dan shekara 12, wadanda ke zanga-zangar lumana a daidai lokacin da ake fama da rikicin kabilanci a yankinsu.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa tare da takwararta ta kasar Chadi, kungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce a ranar 24 ga watan Janairu, sojoji suka tarwatsa dubban masu zanga-zangar, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu akalla 40.
Kwana guda bayan tashin hankalin ne kuma, a wajen jana’izar wadanda suka mutu, sojoji suka bude wuta kan mutane inda suka kashe karin mutane 10 tare da jikkata wasu akalla 40.
Kungiyoyin na kare hakkin dan Adam sun kara da cewar a jumlace jami’an tsaron Chadi sun kama mutane 212 kuma kuma suka tsare su har na tsawon kwanaki biyar cikin azabtarwa kafin sakinsu.
Wannan rahoto dai ya dogara ne kan hirar da masu fafutukar kare hakkin suka yi da wani adadi na shaidu, likitoci biyu da wakilan kungiyoyin fararen hula, da kuma bidiyo da hotuna, da suka tattara.
Sai dai ministan sadarwa Abderaman Koulamallah, kuma kakakin gwamnatin mulkin sojan Chadi ya musanta cewar sojoji sun bude wuta kan fararen hula, illa kawai kokarin da suka yi don kwantar da tarzomar da masu zanga-zanga suka fara.
Minitsan ya kuma ce kamata yayi a jira sakamakon binciken da gwamnati za ta fitar.