Yakin da Rasha ta ke yi a kasar Ukraine zai iya shafan tattalin arzikin kasar Najeriya a halin yanzu Najeriya ta kan yi sayayyen kayan biliyoyin kudi duk shekara daga kasar Rasha da makwabciyarta.
Yakin zai kawo cikas a cinikin da aka saba, hakan zai iya haddasa tashin farashin wasu kaya a gida.
Najeriya kan shigo da kaya na sama da Naira biliyan 900bn daga kasar Rasha a shekara. Alkaluman hukumar NBS ta kasa suka nuna haka.
Wani rahoto da Punch ta fitar a ranar 1 ga watan Maris 2022 ya nuna cewa daga karshen 2021 zuwa yanzu, an shigo da kayan N993.38bn daga Rasha.
Kasar ta Rasha inda rikici ya barke tsakaninta da Ukraine ta na cikin manyan abokan cinikin Najeriya, ma’ana yakin da ake yi babban barazana ne.
Daga cikin kayan da ake yawan shigowa da su Najeriya daga Rasha akwai kifi, alkama, da sauransu. A karshen shekarar bara, Najeriya tayi wa Rasha cinikin alkama na sama da Naira biliyan 46.
Baya ga haka, Najeriya ta saye kifin biliyoyi daga kasar.
A kan kifi kurum, sai da Najeria tayi wa Rasha cinikin N2.27bn. Baya ga haka, ta sayo magangunan mutane na N4.82bn a watanni ukun karshen 2021.
Abubuwa sun fara yin kasa Kafin shigowar shekarar nan, Rasha ce ta biyar a jerin kasashen da Najeria ta ke sayen kayansu.
NBS ta nuna cewa matsayin kasar ya sauko zuwa na shida.
Haka zalika alkaluman majalisar dinkin Duniya na cinikin kasa da kasa sun nuna Najeriya ta kashe $156.08m a sayo kaya daga Ukraine da aka aukawa.
Masana su na ganin cewa alakar kasuwancin da ke tsakanin Najeriya da wadannan kasashe zai ragu sosai a ‘yan kwanakin nan saboda yakin da ya barke.
Najeriya ta saba sayen mai, karafuna, takin zamani daga wadannan kasashe. Idan ba ayi dace ba, yakin zai iya jawo tashin farashin wadannan kaya a gida.
Ukraine ta rasa sojoji 130 Tun a makon jiya aka ji Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce akalla sojojinsa 137 aka hallaka a sakamakon barkowar da sojojin kasar Rasha.
Baya ga haka, Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa sojojin kasarsa 316 sun samu rauni a hare-haren. Yanzu kasashen biyu su na kokarin su cin ma maslaha.