Mutanen kashmir sun fito kwan su da kwarkwatar su kan titi domin nuna tsananin rashin amincewar su da kona hoton janaral kasim sulaimani da wani soja yayi.
Tun asali mutanen garin magam walwali wanda yana yankin kashmir kuma suna karashin mulkin mallakar indaya, sun bayyana bacin rai ne sakamakon sojan lokacin yana binciken gidaan wani mutun ya ga hoton janaral kasim sulaimani makale a jikin bango inda ya ciro hoton kuma ya cinna masa wuta lamarin daya harzuka al’umma wannan birni kuma suka fito mazan su da matan su domin nuna bacin ran su da wannan ta’addanci da aka gabatar a kan hoton babban janaral kasim sulaimani diin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu hatsaniya mai yawan gaske a birnin na magam walwali wanda hakan ya tilasta tsayawar komi a birnin, inda aka samu karo tsakanin mutanen gari da jami’an tsaro.
Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa ba’a samu asarar rayuka sakamakon lamarin amma an samu masu raunuka da dama, sa’anna duk da takurawa da jami’an tsaron sukayi mutanen wannan gari basu koma gidajen su domin a cewar su ba za’a aiwatar da wannan ta’addanci a kan janaral sulaimani kuma basu dauki matakin daya dace ba.
A karshe dai jami’an tsaro a wanna gari sun nemi sulhu inda suka nemi gafara bisa wannan babban laifi da daya daga cikin su yayi kuskuren aikatawa kuma suka dauki alkawarin hukunta shi kamar yadda ya dace.
Shugaban sojojin wannan gari ya bayyana a gaban jama’a dauke hoton janaral kasim sulaimani gami jagoran juyin juya hali na Iran Ayatullah Sayyid Khmane’e duk a wani mataki na hakurkurtar da al’ummar wannan gari.
Bayan nan duka dai a matakin bada hakuri jami’an tsaron sun shiga cikin mutanen gari inda aka lillke layukan birnin da hotunan janaral kasim sulaimani da kuma na jagora sayyid khamne’e.
Hausawa dai sukayi ”Gaskiyar Mutum Bata Daba Karewa Ba”