Wasu alkaluma da kamfanin dillancin labaran Faransa ya tattara, sun nuna yadda cikin watanni 5 hare-haren bindiga dadi suka yi sanadin mutuwar mutane dubu 17 ciki har da kananan yara 650 a sassan Amurka.
Alkaluman da AFP ya tattara na nuna cewa ana kashe mutum 111 kowacce rana a sassan kasar ta Amurka, wanda ya mayar da jumullar mutanen da ke rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren bindigan zuwa dubu 41 kowacce shekara.
A cewar kungiyar Everytown zuwa yanzu makamantan hare-haren ‘yan bindiga dadi ya karade ko’ina a sassan Amurka inda a jihar Texas da ke da kwarya-kwaryar dokar sayar da makamai ke ganin mutuwar mutane akalla dubu 3 da 600 duk shekara sanadiyar harin bindigar.
Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu akalla mutane dubu 17 da 199 hare-haren bindigar ya yi sanadin mutuwarsu ciki har da dalibai yara 19 da malamansu 2 da wani dan bindiga ya harbe a wata makarantar firamare da ke jihar Texas a jiya laraba.
A shekarar 2021, fiye-fiye da mutane dubu 45 suka mutu a hare-haren bindiga cikin sassan kasar ta Amurka, ciki har da kisan gilla dubu 20 da 920 wanda ke matsayin mafi kololuwa da aka gani tun bayan shekarar 2017 lokacin da mutane dubu 58 suka rasa rayukansu sanadiyyar irin wadannan hare-hare.
Alkaluman sun kuma yadda cikin watanni 5 aka samu mutane dubu 14 da samu muggan rauni a sanadiyyar harin bindigar, wanda galibi ke da nasaba da nuna wariya.