Mutane da dama daga jma’iyyun siyasa daban daban ne ke shirin kalubalantar Emmunel Macron a zaben shugabancin kasar Faransa wanda za’a yi ranar 10 ga watan afrilun shekara mai zuwa.
Marine Le Pen daga jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi wadda ta sha kaye a zaben 2017, na daya daga cikin mutane ‘yan takara a zaben mai zuwa.
Sai kuma wani tsohon minista mai suna Xavier Bertrand na jam’iyyar Les Republicans wanda shine yana cikin mutane ‘yan takara, ga kuma Michel Barnier wanda ya jagoranci tawagar Tarayyar Turai don tattaunawar yanjewar Birtaniya daga gungun Turai da ake hasashen cewa shi ma za tsaya takara a zaben.
Tuni dai Yannick Jadot na jam’iyyar masu fafutukar kare muhalli ya yi nasarar lashen zaben fidda gwani don tsaya wa jam’iiyar, yayin da a hannu daya akwai Jean-luc Melenchon wanda ya taba tsayawa a zaben shekara ta 2017.
A bangaren mata kuwa akwai Valerie Pecresse, sai Anne Hidalgo magajiyar garin birnin Paris da ke fatar tsayawa takara karkashin inuwar jam’iyyar socialist.
A wani labarin na daban gwamnatin Girka ta kulla wata yarjejeniya da Faransa don samar mata da jiragen yaki guda uku, abin da ake ganin yana cikin shirye-shiryen da Girka ke yi na tunkarar Turkiyya kan rikicin gabar teku da ke tsakaninsu.
Turkiyya wadda tuni da ma ba ta da kyakyawar alaka da kungiyarta NATO, makwafciya ce ga Girkan, na shan suka kan yi wa tsaron yankin da na kasashe makotanta barazana.
A cewar Firaministan Girka Kyriakos, mambobin majalisar tarayyar kasar su 300 sun amince da kulla yarjejeniyar cinikayyar jiragen yakin da Faransa, haka kuma shirin ya sami goyon bayan jam’iyyun siyasa biyar na kasar.
A cewarsa, Girka ta lura da irin take-taken Turkiyya na haddasa rikici tsakanin kasashen da ke makwaftaka da ita tun bayan da ta mamaye Cyprus, a don haka ya zama dole ta daura dammarar kare kanta ta hanyar tanadar kayan yaki don jiran ko ta kwana.
Wannan ciniki dai, ana ganin zai dan rage wa Faransa raradin da take ji, kan batun kwace cinikayyar jiragen yakin karkashin teku da ta kulla da Ausrtalia da Amurka ta yi.