Akalla mutane 50 da suka hada da kananan yara biyar ne suka mutu a wani hari da aka kai kan tashar jirgin kasa da ke birnin Kramatorsk a gabashin Ukraine.
Kyrylenko ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar adadin wadanda da harin ya rutsa da su zai karu, yana mai cewa har yanzu akwai mutane 98 da suka samu raunuka ciki har da yara 16.
Gwamnan ya ce 12 daga cikin wadanda tashin hankalin ya shafa sun mutu ne a asibiti sakamakon raunukan da suka samu, yayin da aka kashe 38 a nan take.
An dai kai hari kan tashar jirgin kasan da ke Kramatorsk ne da safiyar ranar Juma’a, lokacin da daruruwan mutane suka taru, suna jiran a kwashe su daga gabashin Ukraine inda Rasha ta sabunta kaiwa farmaki.
Sai dai Rasha ta musanta kai harin, wanda ta zargi Ukraine da kaiwa.
A wani labarin na daban Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sanya sunayen ‘ya’yan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin mata biyu da wasu mutane sama da 200 cikin bakin kundi, a wani bangare na sabon takunkumin da ta laftawa kasar Rashan sakamakon mamaye Ukraine da take cigaba da yi.
A jumlace dai kimanin ‘yan Rasha da masu alaka da su 217, kungiyar EU ta sanya sunayensu cikin bakin kundinta.
Dangane da ‘ya’yan shugaba Putin kuwa, da suka hada da Maria Vorontsova da Katerina Tikhonova, tuni dama Amurka da Birtaniya suka sanya musu takunkumi.
Mahaifiyar yaran ita ce tsohuwar matar shugaban Rasha Lyudmila, wadda aka sanar ta rabu da Putin a cikin shekarar 2013.