Akalla mutane 12 suka rasa rayukansu yayin wani turmutsutsu a wajen ibadar mabiya addinin Hindu da ke India da sanyin safiyar yau asabar.
Wani ganau ya shaidawa AFP ta wayar tarho cewa mutane da dama sun jikkata a turmutsutsun yayinda aka kwashe gawar mutum 12.
Rasa rayuwa a wuraren ibadi ko kuma wajen neman tubarraki ba sabon abu ba ne ga mafiya addinin na Hindu wanda ke da rinjayen yawan jama’a a kasar India.
A wani labarin na daban Rundunar ‘yan sandan India ta sanar da fara bincike kan wani taron mabiya addinin Hindu a birnin Haridwar wanda ya tattauna kan yadda za a yi wa Musulmi kisan kiyashi, taron da bayanai ke cewa ya samu halartar wakilcin mamba daga jam’iyyar Firaminista Nrendra Modi.
Faifan bidiyon taron na Hindu ya nuno yadda wani jagora ke bayanin cewa kada mabiyansu su ji tsoron zuwa yari don kawai sun kashe Musulmi, yana mai cewa ba zai zame musu asara ba idan suka sadaukar da mabiyan Hindu 100 don zama sojoji tare da taimaka wa wajen kisan Musulmi miliyan 2 don baiwa wurin bauta na Sanatana Dharma kariya.
Bayanai sun ce, taron wanda ya gudana a tsarkakken birnin Haridwar ya samu halartar guda cikin mambobin jam’iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP wadda ta yi kaurin suna wajen kiyayya ga mabiya addinin Islama.
Sai dai tuni jam’iyyar ta BJP ta musanta batun halartar mambanta ga taron. Kodayake ta tabbatar da sahihancin bidiyon tare da goyon bayan gudanar da bincike a kansa.
Wani fitaccen dan Majalisa kasar Asaduddin Owaisi ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kalaman da ke dauke cikin faifan bidiyon ba komi yak e umarta ba face kisan kare dangi ga mabiya addinin Islama.
Har zuwa yanzu dai gwamnati Modi ba ta yi tsokaci game da taron da kuma fitar faifan bidiyon ba, wanda a cikinsa wata mata ta bukaci mabiyan na Hindu su yi addu’a ga Nathuram Godse wanda ya aikata kisan gilla ga Mahatma Gandhi a shekarar 1948.