Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, musulmi da kiristoci suna yin aiki tare wajen sake gina wani tson masallaci da aka gina shi daruruwan shekaru da suka gabata a lardin Alminya a kasar Masar.
Daya daga cikin masu jagorantar aikin sake gina wannan masallaci ya bayyana cewa, wannan masallaci yana daga cikin tsoffin wurare na tarihi da yankin, amma an wayi gari masallacin an kaurace masa saboda rashin kula da lalacewar gininsa.
Wani mutum daga cikin dattijan garin mai Imad Shuhat wanda kirista ne, shi ne ya bayar da shawara kan cewa ya kamata a sake gyara masallacin, kasantuwar cewa yana daga cikin muhimman wurare na tarihi na musulmi da suke yankin.
Wannan shawara ta samu karbuwa a wurin musulmi da kuma mabiya addinin kirista, a kan haka suka hadu baki daya suna gudanar da aikin sake gina wannan tsohon masallaci.
A wani labarin na daban kuma tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Masar sun sanar da cewa, rufe wannan mashigar yana da alaka ne da shiga tsakanin da Kasar Masar take yi tsakanin Isra’ila da kuma kungiyar Hamas.
Haka nan kuma wani daga cikin jami’an gwamnatin kasar ta Masar ya ce, an dauki wannan matakin ne da nufin yin matsin lamba a kan kungiyar Hamas dangane da batun dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila, kamar yadda kuma ya bayyana cewa ba a san har zuwa wane lokaci ne mashigar ta Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe ba.
Mashigar Rafah dai ita ce babbar mashigar da ake shigar da kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin Zirin Gaza, wanda Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza suke yin amfani da ita domin ci gaba da rayuwa.
Gwamnatin kasar Masar tana yin amfani da mashigar Rafah domin yin matsin lamba akan Falastinawa musamman ma kungiyoyin gwagwarmaya na yankin zirin Gaza, inda ta kan rufe wannan mashiga a duk lokacin da ta ga dama, domin yin matsin lamba a kansu domin su amince da wasu bukatu na Isra’ila ko kuma wasu kasashen na daban.