An dakatar da Jose Mourinho daga halartar wasanni biyu, bayan da a ranar Talata alkalin wasa ya bashi jan kati saboda bacin ran da kocin ya nuna yayin wasan da AS Roma ta yi da Verona a gasar Seria A.
Kafofin yada labaran Italiya sun ruwaito cewa Mourinho bai ji dadin yadda aka kara lokaci kadan ba a ranar Asabar, yayin wasan da aka tashi 2-2 tsakanin kungiyarsa ta AS Roma da Verona.
A yanzu Roma ta koma tazarar maki shida tsakaninta da Juventus wadda ke matsayi na hudu a gasar zakarun Turai.
A wani labarin na daban Wata Babbar kotu a Najeriya ta baiwa Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA umurnin ci gaba da tsare Mukaddashin kwamishinan ‘Yan Sandan Abba Kyari na karin kwanaki 14 domin gudanar da cikakken bincike akan tuhumar da ake masa na taimakawa masu safarar kwayoyi.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta amince da bukatar Hukumar domin bata lokacin gudanar da bincike akan zargin.
Bani da lafiya – Abba Kyari
Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sandan Abba Kyari ya shigar da kara kotu inda yake bukatar ta bashi damar amfani da dokokin kasa wajen kare hakkokin san a Bil Adama wajen sakin sa daga inda ake tsare da shi saboda dalilan rashin lafiya da suka hada da cutar suga da hawan jini, amma mai shari’ar ta dage sauraron karar zuwa ranar alhamis mai zuwa.
A makon jiya ne Rundunar Yan Sandan Najeriya ta kama Abba Kyari ta kuma mikawa Hukumar NDLEA wadda tayi shelar neman sa ruwa a jallo, bayan yaki amsa gayyata domin bada ba’asi dangane da zargin da ake masa na alaka da masu safarar kwayoyi.
Bidiyon zargin Abba Kyari
NDLEA ta gabatar da wani faifan bidiyo dake nuna Kyari na tattaunawa da wani jami’in ta akan yadda zasu raba wata hotar ibilis da aka kama a tashar jiragen Enugu bayan an shiga da ita kasar daga Habasha.
Wannan kamu ya haifar da cece kuce a ciki da wajen kasar saboda danganta shi da Kyari wanda ake gani a matsayin daya daga cikin jaruman rundunar Yan Sandan Najeriya dake yaki da masu aikata manyan laifuffuka.