Manyan kasashen duniya sun fara mayar da martani kan nasarar kashe daruruwan ‘yan ta’adda da sojojin Mali ke ikirarin samu nasarar yi a yankin Moura, inda a ranar Juma’a tsohuwar uwargijiyar Mali wato Faransa ta bayyana shakku kan gaskiyar wannan ikirarin.
Le Drian ya kuma bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya domin gano gaskiyar al’amarin da ya faru a yankin Moura.
Sai dai a yayin da Faransa ta bayyana na ta matsayin, Rasha kuwa jinjinawa dakarun kasar Mali ta yi bisa nasarorin da suke samu kan ‘yan ta’adda, bayan kashe mayakan masu ikirarin Jihadi fiye da 200 da suka yi cikin ‘yan kwanaki a yankin Moura, nasarar da Rasha ta bayyana a matsayin gagaruma.
A wani labarin na daban ‘Yan kasar Mali sun gudanar da gamgani ranar Asabar a birnin Bamako domin murnar ficewar sojojin Faransa daga kasar Mali, a wani yunkuri na nuna goyon baya ga mahukuntan rikon kwaryar da sojoji suka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP yace wasu daruruwan mutane ne suka hallara dandalin ‘yancin kai, dake tsakiyar babban birnin kasar Mali, domin nuna goyon bayarsu ga matakin gwamnatin sojin kasar.
Sai da gangamin bai hada mutane sosai kamar yadda aka gani a baya ba, wato yayin zanga-zangar goyan bayan juyin mulki da sojoji sukayi sai biyu a watan Agusta shekarar 2020 sannan a watan Mayu 2021, inda dubban mutane suka taru a Bamako.
Makomar dakarun Majalisar Dinkin Duniya
Faransa da kawayenta na Turai sun tsara janyewar sojojinsu daga Mali a ranar Alhamis, lamarin da ya sa sauran kasashen ketare suka fito fili suka nuna shakku kan kudurinsu, da kuma tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali (Minusma) ke nazari kan tasirin wannan janyewar.
Watsi da shirin zabe
Gwamnatin mulkin soji a Mali ta yi watsi da alkawarin da ta dauka na gudanar da zabe a watan Fabrairun 2022 domin komawar farar hula kan karagar mulki. Ta yi kira da a samar da sauye-sauye mai zurfi tare da jajircewa kan ikon mallakar kasa tun bayan da kasashen Afirka ta Yamma suka kakabawa Mali takunkumi mai tsanani na tattalin arziki da diflomasiyya a ranar 9 ga watan Janairu.