Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Gana Da Takwaransa Na Siriya.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya yi maraba da tokwaransa na kasar Syriya Faisal Miqdad a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Iran Press IP ya bayyana cewa a ganawar jami’an diblomasiyyar kasashen nan gaba zasu tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma dangane da sakamakon taron Astana na warware rikicin kasar Siriya wanda kasashen Iran Rasha da kuma Turkiyya suka gudanar a jiya.
Tun bayan da aka kawo karshen ikon yan ta’adda a mafi yawan kaasar Siriya a shekara ta 2017 ne aka dorawa kasashen uku nauyin bin al-amuran da ke faruwa a kasar Siriya da kuma warware matsalolin da suka rage a kasar.
A halin yanzu dai kasar Rasha tana da sansanin sojojinta a kasar Siriya tare da amincewar gwamnatin kasar tun zamanin mahaifin shugaban kasa mai ci wato Hafizul Asad.
READ MORE : Gudanar Da Zaben Raba Gardama A Kasar Falasdinu Ita Ce Mafita A Riki Kasar Da Aka Mamaye-Abdullahiyan.
Ana saran bayan ganawar jami’an diblomasiyyar guda biyu, zasu yi hira da kafafen yada labarai da yan jaridu don bayyana musu inda aka kwana a tattaunawanAstana, da kuma dangantaka tsakanin kasar biyu.