Cire saƙonnin da aka yi a ranar Laraba ya janyo ƙorafe-ƙorafe daga gwamnatin Malaysia, wacce ta yi gargaɗin ɗaukar tsauraran matakai kan kamfanin Meta da sauran kamfanonin sadarwa na intanet.
Malaysia ta daɗe tana rajin ganin an samar da ƙasashe biyu don warware rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.
Kamfanin kafofin sadarwa ta intanet Meta ya maido da saƙonnin Facebook da kafafen yaɗa labaran Malaysiya suka tattaro daga ganawar da Firaministan ƙasar Anwar Ibrahim ya yi da wani shugaban ƙungiyar Hamas a cikin makon nan, yana mai cewa an cire su ne bisa kuskure.
“An cire wasu saƙonni biyu cikin kuskure, kuma yanzu an dawo da su,” a cewar saƙon imel da wani mai magana da yawun Meta ya aika wa kamfanin dillacin labarai na Reuters a ranar Alhamis.
Anwar ya gana da Ismail Haniyeh na ƙungiyar Hamas a Qatar a ranar Litinin.
Ya jaddada cewa duk da cewa yana da kyakkyawar alaka da shugabannin siyasa na ƙungiyar, amma ba shi da hannu a ɓangaren harkokin sojinta.
Daga bisani, Malaysiya ta aika da wata wasiƙa tana mai neman Meta ya yi ƙarin bayani kan cire saƙonnin a kafafen yada labaranta biyu kan batun ganawar da kuma rufe wani shafin Facebook na kafar Malaysiya Gazette, wacce ke yaɗa al’amuran da suka shafi Falasɗinu a watan da ya gabata.
Ministan Sadarwa na Malaysiya Fahmi Fadzil, wanda kuma shi ne mai magana da yawun gwamnati, ya yi Allah wadai da cire saƙonnin, yana mai zargin ƙungiyoyin Amurka da rashin mutunta ‘yancin kafafen yaɗa labarai.
Kafar yaɗa labarai ta Malaysiya Gazette ta faɗa a ranar Laraba cewa ta roƙi Facebook ya sake buɗe mata shafinta kuma ya amince, a halin da ake ciki yanzu shafin ya fara aiki.
Hana duk wani shiri da ke goyon bayan Falasdinu
Malaysiya tana goyon kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta da kuma ‘yantar da ƙasar ta hanyar samar da ƙasashen biyu bisa ga yarjejeniyar iyakoki ta 1967 tare da Gabashin Kudus wanda a halin yanzu ke mamaye a matsayin babban birninta.
Kazalika, ta buƙaci a ba Falasɗinu damar samun cikakken matsayi na mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
Meta dai ya bayyana cewa ba da gangan yake goge muryoyi a dandalinsa na Facebook ba, yana mai cewa ”babu gaskiya” kan zargin da ake yi na taƙaita abubuwan da suka shafi goyon Falasɗinawa.
Meta ta ayyana Hamas, ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa da ke mulkin Gaza, a matsayin “kungiya mai matukar haɗari” tare da haramta duk wasu abubuwa na nuna goyon bayan ƙungiyar.
Haka kuma yana amfani da fasahar bincike daban-daban na kai tsaye da kuma bita na ɗan adam wajen cire ko kuma goge hotuna da ke da alaƙa da ƙungiyar.
A farkon wannan watan ne, ma’aikatan kamfanin Meta suka wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa inda suka soki yadda kamfanonin ke yin katsalandan a cikin gida da waje kan nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
DUBA NAN: Taron Yaki Da Wariyar Launin Fata Ga Falasdinawa A Afrika Ta Kudu
Kazalika, wasiƙar ta ce kamfanin ya cire “duk wani goyon baya ko tallafi a fili ga abokan aikinmu na Falasɗinu ko kuma miliyoyin da ke fuskantar matsalar jin kai a Falasɗinu” a kan dandalin kamfanin.